NI AYS NAKE SO Part 1 to 2

[8:52AM, 9/25/2017] ��Eshat aysm��: ������
      �� *NI AYS NAKESO*��
                 ������

.

*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
_We dont just entertain and educate we also touch the herts ƙf readers_

.

.



_WRITEN BY Princess Eshat Aysm_

.

.

In Dedication to *ABDULLAHI YAHYA SA'AD ZARIYA*
A.Y.S



Page 1

.




Wani irin tsawa aka buga dayasa hanjin cikin ta murɗewa, ta ɗaga ido taga sama tayi bak'ik'irin, tsoro ya kamata gashi tayi nisa akusa da mutane, nan take ta fara kuka tana danasanin fitowa, wani tsawan aka sake bugowa, ta runtse ido tana tunanin a ina zata samu abun hawa, sai da Ammi ta hanata fita amma tayi taurin kunne, wani kukanne ya kufce mata ta fara shek'a shi da iya k'arfin ta.
kamar daga sama taji hoon ɗin mota abayan ta, da sauri ta juya, ganin glass ɗin motar me duhu ne bata ganin naciki yasa ta runtuma da wani mahaukacin gudu.
Jan motar akayi akaci gaba da binta, sai gudu takeyi tana kuka, "yau nahaɗu da 'yan yankan kai Allah ka tsareni, gashi ba kowa yau nashiga uku".
gwaruwa tayi da wani garu yasa dolenta ta tsaya, Motar ne ta nufota, ya buɗe murfin motar yafito, sai yanzu ta daɗa razana, ta tabbatar wannan kam ba mutum bane saboda kyawun shi ya wuce na mutane, ta waro ido da hanci tana kallon inda yake nufo ta, dogone fari k'al dashi, hancinsa kamar pencil, ga wani rami a gefen kumatunsa (Dimples).

tsugunawa tayi a wajen tana kwararo addua, har gaban ta ya k'arasa ya tsaya, "Ni ban gudu miki ba sai ke zaki gudumun, kalli sama, wannan ruwan ya sauk'o zai iya tafiya dake shikenan kin mutu, shi yasa na tsaya zan temake ki".
Tunda ya fara magana take kallon ɗan mitsitsin bakin shi, maganar ma dagani a dole yake, cikin tsoro ta ce "kana nufin kai ba Aljani ba ne"?
Dariya ta bashi har dimples ɗinshi suka lotsa, ya ce "kin taɓa ganin aljani ne? Su ai dukkanin su munana ne, ni kuma ya kika ganni".
ya kashe mata ido
"kafin tayi magana ruwa ya sauk'o da k'arfi sosai, ko ganin gabansu basuyi saboda inda hadirin ya rufe wajen.

Lalume ya fara yi har yaji ya rik'o hannun ta, wani k'ara ta saki duk a razane take, ya janyo ta da k'arfi ta faɗa k'irjinsa, dai2 lokacin akayi wani walk'iya me hasken gaske, motarsa ya hango yayi saurin janta suka shiga ciki, sai a lokacin ya sauk'e ajiyan zuciya, ya juya ya dubeta sai ɓari takeyi, wani k'aton rigar sanyi ya janyo a sit ɗin baya, ya  mik'a mata yace  " sanya wannan, amma ki cire jik'akken tukunna".
Kallon shi tayi daga sama har k'asa "Basshi kawai na gode".
Ganin haka yasa yafuta a motar ya rufo, ruwa yaci gaba da dukansa, "to shi wannan mutumin bayajin sanyi ne, oho mishi shi yaso".
Ta faɗa tana karkaɗa rigar, najikin nata ta cire ta saka na sanyin, harda k'aton hula a jiki, lokaci guda ta nemi sanyin ta rasa, har wani ɗumi takeji yana shigar ta.

ɓuɗewa yayi ya shiga, fuskanshi yana kanta, lokaci guda kuma ya kauda kai ya tada motar "Ina zan kaiki".
ya tambaya hankalin shi nakan tuk'i, taɗan zaro ido "basai ka kaini ba nagode, idan ruwan ya ɗan tsaya zan tafi babu nisa".
Bai kalle ta ba ya ce "baki bani amsaba fa".
Aranta tace "yanzu me nabaka idan ba amsa ba".
Kallon shi tayi tace "kayi hak'uri".
da sauri ya kalle ta "amsar kenan"?
Ta ce "eh".
tada motar yayi ya ɗau hanya "idan nakai ki gidanmu ai zakiyi magana me kyau".
ware ido ta sake yi "a'a tsaya zan faɗa maka, amma idan anganni a motar nan zansha duka".
yace "karki damu, namiki alk'awarin bawanda zai bugeki".
kwatance ta masa gidanmu yana bayan NITEL a nesa zaka ajiyeni".
Bai ce mata kome ba, sun ɗanyi nisa ta ce "kai bakajin sanyi ne"?




"inaji lokacin da naga kina ɓari, amma da kika saka rigarnan sai naji nadaina ji, inaga jininmu iri ɗayane".
"uhm". kawai tace.
Ba wanda ya sake magana har suka iso anguwar, da hanu tayi ta masa alama har suka isa k'ofar gidan, da hanzari ta buɗe motar zata fita ya dakatar da ita "ke agarin ku haka akeyi".
Tayi dariya ta ce "kayi hak'uri mantawa nayi, nagode, sunana AISHA".
murmushi yayi ya ce "bance kimun godiya ba, Sunan ki na tambaya, naga kina farinciki kin shiga motar kyakkyawa ko"?
Dariya ya bata aranta tace "shima yasan yanada kyau".
Ta kalleshi ta ce "ina wani kyau mutum yana kama da aljanu".
Dariya yayi sosai ya ce "sunana UMAR MUHAMMAD, zaki iya k'irana faruq".
"suna me daɗi na gode da taimako".

Buɗe motar tayi da fara'arta ta nufi gida, gaban tane yafaɗi ganin mahaifin ta a tsaye, dayake lokacin ruwan ya tsaya, juyawa tayi ta kalli motar Faruq tunawa da tayi yamata alk'awarin baza'a daketa ba, yananan a wajen amma bata ganinshi, dak'yar ta k'arasa, tun kafin yamata magana tafara rantse2, "Abbahna ruwane yamun duka wlh taimaka mun yayi....
cikeda ɓacin rai yace "na tambaye ki, shiga motar wani shine kin kare kanki, kada ruwa ya dakeki, kinsan hatsarin da shigar yake nufi"?
Bakinta na rawa tace "Nasani Abbah".
Duk tagama jiɗimewa, tasanshi sarai ya tsani yaganta tana hira balle ace ta shiga motar wani, kullum sai yayi mata gargaɗi, bata jira me zai sake faɗaba tayi cikin gidan da gudu.

Faruq yana kallonsu, mezaiyi inba dariya ba, yarinyar nan gaba ɗaya matsoraciya ce, ahankali ya fito a motar har ya iso gaban Abbah ya tsuguna ya gaishe shi.

A dak'ile Abbah ya amsa, Faruk ya sunkuyar dakai ya ce "ruwane naga zai mata illah, ban ɗauko ta da wani manufa ba, kayi hak'uri dak'yar ta yadda ta shiga ma".
Tun tsugunawar sa Abbah ya lura yaron kamili ne, ya masa k'warjini sosai, hanu ya ɗaga masa ya ce "na gode".
Juyawa yayi ya nufi cikin gidan Faruk ya bishi da kallo yana tunanin tsaurin ra'ayi irinna Abbah.






.

.
[8:15AM, 9/27/2017] ��Eshat aysm��: ������
      �� *NI AYS NAKESO*��
                 ������

.

*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
_We dont just entertain and educate we also touch the herts ƙf readers_

.

.



_WRITEN BY Princess Eshat Aysm_

.

.

In Dedication to *ABDULLAHI YAHYA SA'AD ZARIYA*
A.Y.S



Page 2

.









.

.











Da gudu ta shige ɗaki tana neman Ammi, ganin bata nan tayi ɗakin su Hajara da gudu, suna ganin ta suka tintsire da dariya, Sadiya ta ce "waye ya koro ki, ruwa ya miki duka ko"?
B'ata rai tayi "kunsan bana son tambayoyi, mik'omun wayata".
"Aunty a ina kika samo wannan rigar"?
Hajara ta faɗa tana k'unshe dariya, harara ta sakar mata ta ce "Nidai nashiga uku, ku kenan ba dama kuga abu sai kuyi ta damun mutane, to na Faruq ne".
Me zasuyi inba dariya ba, sun santa sarai idan batada gaskiya tayi ta ɓata rai kenan tana tsare gida, tunanin su ya tafi akan Abbah ya bugeta ne, wayar ta fizge a hanun Sadiya, "Bani nahau Facebook, nasan masu sunan 'yan gayun nan sun turo kalamai masu daɗi".
dukan su suka matso kusa da ita, Sadiya ta ce "kullum ke group ɗaya kike shiga, yau kam kishiga mana wani".
Dariya Aisha tayi ta ce "sai dai kuyi zuciya a fara barinku kuna rik'e waya, wannan tsaurin Boss ɗin namu bazai bari mutum yaɗan me rayuwa take cikiba".
Hajara tayi tsaki "ni kiyi kishiga mana".

Login facebook tayi, an cika mata inbox da sak'o amma ko dubawa batayi ba, Grup ɗin 'yan gayu ta shiga, *ABDULLAHI YAHYA SA'AD ZARIA*
Kullum sunan da take gani yana shawagi kenan a group ɗin, mssg yake turowa masu zafi na love, yau kam bataga post ɗinshi ba, ta dudduba duk babu na yau, sai tsirarrun post ɗin da akayi shima duk tambaya ake yau bamuga AYS ba.
Hajara ta ce "to waye kuma AYS"?
"oho musu, inaga ita macece, ni Abdullahin nan yana masifar burgeni, ni duk inda nashiga sunanshi ake ambata, da alama yaron yanada farinjini, kuma yanada baiwa, yanada tarin masoya amma bashida girman kai, ko inane zarian oho".
Sadiya ta ce "ke zarian ma baki sani ba, anbarki a baya".
Tashi tayi tana cewa "zan lek'a ammi ko ta fito daga wanka, Hajara kije ki zubo mana abinci yanzu zan dawo".
Duk sukayi waje, Aisha kam wayar tata ta zubawa ido, sosai takejin kewar Abdullahi, yau me yahana shi hawa, Allah yasa lafiya, rigar jikin ta ta kalla tayi dariya "wannan kuma ɗan rigimar nabar rigata a motar sa, yanzu hakama ya yar mun, hmmm amma gaskiya kyakkyawa ne, Allah kada kabani mijin da yafini kyau, 'yanmata suna bibiyan shi hawanjini ya kamani, shi dakanshi ma gori zaimun tabɗi Allah ya tsareni".

Mik'ewa tayi tashiga wanka, tana fitowa tasaka kayan Sadiya riga da zani, ko iya ɗaura zanin batayi ba balle ɗankwalin, haka dai ta murɗa ta ɓoye wayar ta tayi ɗakin Ammi itama.

AMMI macece hamshak'iya, sam batada k'awayen da suka wuce 'ya'yanta, suma yaran kansu a haɗe yake, komai a tsakanin su sukeyi ba ruwansu da k'awaye, idan ɗaya yana cikin matsala to tamkar dukansu ne, MUHAMMAD MESAJE shine mahaifinsu, irin mazannan ne masu tatssauran ra'ayi, bayaso yabada doka a tsallake, magana ɗaya yakeyi baya canzawa, yaran su 5 ne, AISHA, SADIYA, HAJARA, AL'AMIN, ABDU, JAFAR.
Babu abunda suka nema suka rasa kullum cikin Farinciki suke rayuwa.








.
.
.
.
.
.



Faruq tunda yaɗau hanyar gida yaketa dariya shi kaɗai, "wannan yarinyar tayi mun sosai, zankai wa Momcy labari".
Yana isa kamfacecen gidan su yayi hon, da sauri me gadi yazo ya buɗe, saida yazo futa ya hango rigar ta da hijabin ta, nurmushi yayi ya ɗauko, k'amshin ta ya bugi hancinsa, ya lumshe ido yana murmushi, ɗakin shi ya nufa yajefa kayan a mchn na wanki, sannan yayi wanka ya nufi ɗakin mahaifiyar shi, jikin ta yaje ya kwanta yana zunɓura baki, ta shafo kanshi ta ce "Babana ina kashiga".
"yau ko sau ɗaya baki k'irani ba".
"sorry my son, netwk ne babu kyau, ina fata babu abunda ya taɓa mun kai".
Cikin zumuɗi ya ce "Akwai Momcy, wata yarinya ta taɓamun zuciya, na kamu da sonta Mom".
Mamaki gami da farinciki ya kama Mom, kullum adduan ta Allah yakawo ranarda zaiga yarinyar dayake so, babu irin matan da ba'a kawo mishi ba yace baiga wacce tamishi ba, yau Allah yayi, rungume shi tayi tana sa mishi albarka, "Nayi murna Babana, ka gayya to abokanka zan shirya muku Fati na murnar ganin yarinyar da kake so".
"woooo lov u Momcy Allah yabarmun ke a raye".
dariya tayi.






Tace "maza tashi kaje kaci abinci, idan nabarka haka zaka kwana".
Cikin farinciki yake don haka babu gardama ya tashi.


UMAR FARUQ mahaifin shi ya rasu yanada shekaru 15, shi kaɗai suka haifa, don haka Momy taɗau son duniya ta ɗaurawa Faruq, sauda yawa sai tayi tunanin tayi aure sai taga duk kuɗin ta suke so, don haka ta hak'ura ta rik'e ɗanta tilo.


Post a Comment

0 Comments